IQNA

Manyan malaman addini na Damascus sun gana da shugaban kasar Iran

17:12 - May 05, 2023
Lambar Labari: 3489089
Tehran (IQNA) Sayyid Ibrahim Raisi, shugaban kasar Iran a yau 14 ga watan Mayu a wani bangare na ziyararsa a kasar Siriya ya karbi bakuncin ministan Awka na kasar Abdul Sattar Al-Sayed da tawagar manyan malaman addini na Damascus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yayin wannan taro, manyan malaman addini na birnin Damascus, a yayin da suke maraba da zuwan  Raisi a kasar Siriya, sun jaddada muhimmancin dangatakar da ke tsakanin Damascus da Tehran, wajen tunkarar ta'addancin Amurka da yahudawan sahyoniya. A cikin tsari guda, wanda ke shafar yankin da dukkan al'ummar Larabawa da na kasashen musulmi.

Manyan malaman birnin Damascus sun bayyana a cikin wannan taron cewa tsayuwar daka na shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya kawar da dukkanin makirce-makircen takfiriyya da ta'addanci da makirce-makircen kasashen yamma karkashin jagorancin Amurka da Isra'ila.

A cikin wannan ganawar, shugaban na Iran ya kuma mika godiyarsa ga manyan malaman birnin Damascus tare da jinjinawa zaman lafiyar shugabanni da al'ummar kasar Sham, sannan ya bayyana goyon bayan Iran da kuma tsayin daka a gare su.

Ya jaddada zurfin da karfin dangantakar da ke tsakanin Tehran da Damascus, da kwanciyar hankali da kwanciyar hankali na dukkan kasashen yankin.

A karshe shugaban na Iran ya jaddada cewa matakin tsayin daka da shugaba Assad ya dauka ne ya sa kasar Siriya ta samu galaba akan ta'addanci da kuma magoya bayanta.

 

 

4138575

 

captcha