IQNA

Cibiyar Hubbaren Abbasi ta sanar da cewa;

Kasashe 16 ne suka halarci rubutun kur’ani na masu ziyarar Arbaeen

19:55 - November 05, 2022
Lambar Labari: 3488128
Tehran (IQNA) Majalisar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta Cibiyar Hubbaren Abbasi  ta sanar da halartar mahajjata maza da mata 1750 daga kasashe daban-daban 16 don rubuta kur'ani mai tsarki da masu ziyarar  Arbaeen suka rubuta a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Kafil cewa, majalisar kula da harkokin kur’ani ta Cibiyar Hubbaren Alawi ta gabatar da kwafin karshe na kur’ani mai tsarki na masu ziyarar Arbaeen Hosseini ga Sayyid Ahmed Al-Safi, ma’aikacin wannan kofa.

Shugaban majalisar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta Cibiyar Hubbaren Abbasi  Mushtaq Al-Ali ya bayyana cewa: Da nufin karfafa al'adun kur'ani mai tsarki a tsakanin kungiyoyi daban-daban na al'umma da kuma bisa dabarar hangen nesa na majalisar ilimin kur'ani mai tsarki an fara wannan taro rubuta Alqur'ani da rubutun hannun masu ziyarar hajjin Arbaeen.

Ya kara da cewa: Rubutun da aka yi amfani da shi a cikin wannan kur'ani shi ne rubutun da aka yi amfani da shi a Mushaf na Haramin Abbasiyya, kuma an aiwatar da wannan aiki ne da nufin karkata ayyukan ruhi da al'adu da ilimi ga masu ziyarar da suka zo Karbala.

Shi ma shugaban cibiyar buga kur’ani ta hubbare Alawi Sheikh Ziauddin Zubeidi ya ce dangane da haka: Ana kiran wannan kur’ani mai suna “Mushaf Samra Arbaeen da hannuwan masu ziyara” kuma Sayyid Ahmad Safi, sakataren Cibiyar Hubbaren Abbasi  ya shiga harkar rubuce-rubucen.

Ya kara da cewa: Masu ziyarar maza da mata 1750 daga kasashe 16 daban-daban ne suka halarci rubuta wannan kur'ani, kuma an rubuta sunayensu baki daya.

4097126

 

 

captcha