IQNA

Wata Tawagar Malaman kur'ani Daga Mauritania Ta Kai Ziyara A Cibiyar Kur'ani Ta Hubbaren Imam Hussain (AS)

22:40 - November 17, 2021
Lambar Labari: 3486572
Tehran (IQNA) wata tawagar malaman kur'ani daga kasar Mauritaniya ta kai ziyara a cibiyar kur'ani ta hubbaren Imam Hussain (AS)

Kamfanin dillancin labarai na qaf ya bayar da rahoton cewa, a yau wata tawagar malaman kur'ani daga kasar Mauritaniya ta kai ziyara a cibiyar kur'ani ta hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin karbala na kasar Iraki.

A cikin wannan tawaga ta masu karatu akwai malamai kamar su Sheikh Salman Ahmad Sal, Sheikh Tiran Tiran Saleh da Bobo Kan, sun kuma ziyarci gidan rediyon hubbaren Imam Husaini (AS), a cikin shirin "da Rattle Al-Qur'an" wanda Malam Ali Al-Khafaji ne ya gabatar da shi kai tsaye, inda ake gabatar da malamin kur'ani, kamar yadda kuma aka gabatar da wadannan baki.

Mambobin tawagar kur'ani ta Mauritaniya sun tattauna kan hadin gwiwar ayyukan kur'ani d tare da jami'an da abin ya shafa a hubbaren Imam Hussain (AS)  da kuma yadda ake amfani da hanyoyi na zamani wajen yada ayyukan da suka shafi kur'ani da kuma koyar da shi.

میزبانی آستان مقدس حسینی از گروه قرآنی موریتانی + عکس

میزبانی آستان مقدس حسینی از گروه قرآنی موریتانی + عکس

4013796

Abubuwan Da Ya Shafa: tawaga
captcha