Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wurin adana kayan tarihin rayuwar Annabawa na duniya yana kusa da masallacin Annabi da ke Madina kuma yana bude a koda yaushe ga masu ziyara sa'o'i 24 a kowace rana, kuma an sadaukar da shi don tarihin duniyar Musulunci da kuma tarihin Manzon Allah (SAW).
A wannan wuri ne aka baje kolin manyan rumfuna ashirin da biyar domin nuna kayan tarihi na rayuwar Manzon Allah a Makka da Madina, da kuma kayan tarihi dari biyar masu alaka da zamanin Manzon Allah (saw) a wannan wuri.
Ta yadda maziyartan wannan gidan tarihi na kasa da kasa za su iya ganin abubuwa da suka shafi halaye irin na rayuwar Manzon Allah da tarihinsa.