IQNA

Wata Cibiya A Jordan Ta Saka Jagoran Juyi Na Iran A Cikin Musulmi Masu Tasiri A Duniya

14:37 - October 27, 2021
Lambar Labari: 3486481
Tehran (IQNA) Wata cibiyar a Jordan ta sanya sunayen jagoran juyin na Iran da Ayatollah Sistani da kuma Sayyid Nasrullah a cikin musulmi masu tasiri.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar wadda take gudanar da bincike da take da mazauni a kasar Jordan ta sanya sunayen jagoran juyin an Iran da Ayatollah Sistani da kuma Sayyid Nasrullah a cikin musulmi masu tasiri.

Wannan cibiya tana gabatar da manyan mutane 500 masu tasiri a duniyar Musulunci a kowace shekara tun daga 2009.

A bana dai Jagoran ya zo a matsayi na uku, yayin da Ayatullah Sistani shugaban mabiya mazhabar Shi'a a kasar Iraki ya zo na tara a jerin mutane 10 na farko.

A bisa tsarin ka'idar cibiyar wanda aka buga a shafinta na yanar gizo, manufar buga wannan jerin sunayen ita ce gano sabbin damammaki ga manyan kasashen musulmi, da kuma duk wani musulmin da ta kowace fuska ya fi tasiri a kasarsa.

A kusan dukkanin jerin sunayen da cibiyar ta buga tun daga shekarar 2009, Jagoran ya kasance daya daga cikin manyan mutane biyar a duniyar Musulunci.

 

 

4008222

 

captcha