IQNA

Mai Fasahar Rubutun Larabci Dan Kasar Morocco Ya Kammala Rubuta Kur'ani

22:16 - September 07, 2021
Lambar Labari: 3486283
Tehran (IQNA) Alawah Baitam dan kasar Morocco ne da Allah ya yi masa baiwa ta rubutun larabci, wanda ya kammala rubutun cikakken kur'ani mai tsarki.

Shafin yada labarai Al-sha'ab ya bayar da rahoton cewa, Alawah Baitam  ya dauki tsawon shekaru uku a jere yana rubuta kur'ani da salon fasahar rubutu mai kayatarwa.

Alawah Baitam ya shara a kasar Morocco da salon rubutun larabci iri-iri mai kayatarwa, wanda yake yi a kan abubuwa daban.

An haife shi a garin Ainul Tutah a shekara ta 1958, sannan kuma ya fara hardar kur'ani mai tsarki tun yana da shekaru 6a  duniya, ya kammala hardar kur'ani baki daya yana da shekaru 12 a duniya.

Ya halarci makarantun kur'ani daban-daban, akasarinsu makarantu ne na zawiyya, ko kuma makarantun allo kamar yadda aka fi saninsu a kasar Hausa, wanda irin wadanna makarantu sun samo asali ne dama daga kasashen larabawa na arewacin Afirka.

baya ga rubutun kur'ani, Alawah Baitam ya kasance mai matukar shawa'ar ilimin adabin larabci da kuma abubuwa da suka shafi tarihin larabawa, musamman wakoki da ake tsara su a cikin baituka na hikima.

A kan haka ya yi rubu kan adabin larabawa da tarihinsu da kuma tarihin muslunci a wakoki da yawansu ya kai baitoci 2894, wadanda suke a cikin littafan da ya rubuta  a wannan fage.

 

3995903

 

 

captcha