IQNA

Saudiyya: Jami'an Tsaro Sun Cafke Limamin Jidda Sun Jefa Shi Kurkuku

23:36 - July 05, 2021
Lambar Labari: 3486079
Tehran (IQNA) jami'an tsaron kasar Saudiyya sun cafke limamin masallacin Ummul Miminin Khadijah da ke birnin Jidda sun jefa shi kurkuku.

Tashar Al-alam ta bayar da rahoton cewa, bayan kwashe tsawon lokaci ba a ji duriyar Sheikh Amir Al-muhalhil limamin masallacin Ummul Miminin Khadijah da ke birnin Jidda ba, daga baya ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar ta Saudiyya ne suka cafke shi, suka jefa shi gidan kaso.

Sheikh Amir Al-muhalhil dai yana daga cikin fitattun makaranta kur'ani a  kasar Saudiyya, bayan ga haka kuma shi ne limamin Juma'a na masallacin Ummul Miminin Khadijah Bint Khuwailid da ke birnin Jidda.

Kafin nan ya ya rike limancin wasu masallatan a birnin na Jidda, daga ciki har da masallacin Sarki Faisal da ke Jidda, da kuma masallacin Sanad Al-Ghamidi.

An kwashe tsawon shekara guda ba a ji duriyarsa ba, amma daga bisani ta bayyana cewa jami'an tsaron gwamnatin Saudiyay ne suka yi awon gaba da shi, kuma suke jefa shi kurkuku, saboda ra'ayinsa dangane da salon mulkin yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

Tun bayan da Bin Salman ya yi wa Muhammad Naif juyin mulki, kuma ya dare kan kujerarsa ta yarima mai jiran gadon Saudiyya a shekara ta 2017, daga lokacin ya shiga kame 'ya'yan sarautar kasar da kuma malamai, wadanda suke da sabanin ra'ayi da shi.

Yanzu haka akwai manyan malamai a kasar da Bin Salman yake tsare da sua  gidajen kurkuku, saboda suna yi masa nasiha kan irin salon mulkin da yake yi, wanda suke ganin akwai abubuwa da suka saba wa shari'a ta muslunci a bisa mahangarsu, yayin da shi kuma yake shiga kafar wando daya, ko kuma kawar da duk wanda ya saba wa ra'ayinsa komai matsayinsa a kasar ta Saudiyya.

 

3982148

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kurkuku gidan kaso Cafke Limamin Jidda
captcha