Shafin yada labarai na jaridar The Star ya bayar da rahoton cewa, cibiyar musulmin ta Canada ta bayar da daurin kwalaye dake dauke da tallafin kayan bukatar rayuwa, musamman a lokacin corona da kuma yanayin hunturu.
Rahoton ya ce ciyar ta bayar da wani bangare na taimakon ga cibiyar ayyukan jin kai ta YWCA ta Canada domin raba wag a jama’a mabukata.
Nazem Awwan shi ne bababn daraktan cibiyar ta Yellowknife, ya kuma bayyana cewa taimakon nasu ya hada musulmi da wadanda ba musulmi ba, domin su burinsu shi ne su taimaka ma mutane mabukata kamar yadda addinin musulunci ya yi umarni.
Koa shekarar da ta gabata cibiyar musulmin yankin na Yellowknife ta bayar da tallafi irin wannan ga mabukata a kasar Canada.