IQNA

Zaman Juyayin Ashura Tare Da Halartar Jagora

12:29 - August 30, 2020
Lambar Labari: 3485133
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman juyayin ashura  a husainiyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagora.

Shafin yada labarai na jagora ya bayar da bayanin cewa, a daren jiya an gudanar da zaman juyayin ashura  ahusainiyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagora, inda Hojjatol Islam Rafi’i ya gabatar da jawabi.

Daga cikin muhimman abubuwa da ya yi tsokaci a kansu a yayin jawabin nasa, ya bayyana matsayin dogaro da Allah wanda ya bayyana afili a  cikin aikin Imam Hussain (AS) a ranar Ashura, inda dukkanin barazanar da yake fuskanta bat a iya tsorata shi, bil hasali ma hakan babu abin da ya kara masa sai yakikida abin da ya ji daga bakin kakansa (SAW) domin kuwa a ranar Ashura ne dukkanin abubuwan da aka gaya masa kan yadda za a kashe shi suka tabbata, yana mai imani da Allah da kuma jajurcewa  a kan tafarkin bin Allah da bayar ad kariya ga addininsa.

3919612

 

 

 

 

captcha