IQNA

Wata Tawagar Amurkawa Ta Kutsa Kai Cikin Masallacin Annabi Ibrahim (AS) A Garin Alkhalil

23:53 - February 19, 2020
Lambar Labari: 3484539
Tehran (IQNA) wata tawagar Amurkawa ta kutsa kai a cikin masallacin annabi Ibrahim (AS) garin Alkhalil da ke Falastinu.

A jiya wata tawagar Amurkawa ta kutsa kai a cikin masallacin annabi Ibrahim (AS) garin Alkhalil tare da shiga wasu daga cikin matsugunnan yahudawa da aka gina a cikin yankunan falastinawa a yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran maa ya bayar da rahoton cewa, wannan tawagar Amurkawa ta hada da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican, da kuma wasu daga cikin dangin Trump.

Wadannan Amurkawa sun bayyana cewa manufar ziyarar tasu ita ce duba yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, wadanda dole ne su zama karkashin ikon Isra’ila, kamar yadda Trump ya sha jaddada hakan.

Suka ce dole ne Isra’ila ta zama ita ce take da iko a kan dukkanin yankunan falastinawa baki daya, a kan haka sun zo ne domin su kara jaddada goyon bayansu ga Isra’ila a kan wannan manufa, wadda kuma ita ce babban burin shugaban Amurka Donald Trump.

Bayan kutsa kai a cikin masallacin annabi Ibrahim (AS) da suka yi, sun kuma zagaya a cikin birnin Alkhalil, kamar yadda suka shiga cikin wasu matsugunnan yahudawa biyu da suke kusa da birnin da Birnin domin jaddada goyon bayansu ga yahudawa.

 

3879896

 

captcha