IQNA

Sarkin Sharjah ya Bayar Da Kyautar Kwafin Kur’anai Na Tarihi

23:50 - December 18, 2017
Lambar Labari: 3482211
Bangaren kasa da kasa, sarkin Sharjah a hadaddiyar daular larabawa ya bayar da kyautar wasu dadaddun kwafin kur’anai ga cbiyar kula da kayan tarihi ta masarautar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sharjah24 cewa, Sultan Bin Muhammad Qasimi sarkin Sharjah a hadaddiyar daular larabawa ya bayar da kyautar wasu dadaddun kwafin kur’anai ga cbiyar kula da kayan tarihi ta masarautar ta Sharjah.

Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadannan kwafin kur’anai sun kai imanin shkaru 300 zuwa 400, kuma wasu suna dauke da sharhi na hadisan fikihu tare da su.

Masarautar harja na daya daga cikin masarautu na haddiyar daular larabawa, inda aka n gudanar da taruka na kasa da kasa da suka shafi kur’ani mai tsarki, inda yanz haka aka bude wani baje koli na wadannan littafai da kwafin kur’ani na tarihi a birnin.

Sarkin masarautar Sharjah dais hi ne ya dauki nauyin dukkanin ayyukan da suka danganci adana wadannan kwafin kur’anai a wannan babban dakin ajiye kayan tarihi na addini da ya ke a masarautar ta sharjah.

3673730

 

 

 

 

اهدای نسخ قرآنی چهارصد ساله به دانشگاه شارجه + عکس

اهدای نسخ قرآنی چهارصد ساله به دانشگاه شارجه + عکس

اهدای نسخ قرآنی چهارصد ساله به دانشگاه شارجه + عکس

اهدای نسخ قرآنی چهارصد ساله به دانشگاه شارجه + عکس

 اهدای نسخ قرآنی چهارصد ساله به دانشگاه شارجه + عکس

 

 

captcha