IQNA

Alhazan masar Kimanin 49 Ne Suka Rasa Rayukansu

17:31 - September 04, 2017
Lambar Labari: 3481863
Bangaren kasa da kasa, kimanin alhazan kasar Masar 49 Allah ya yi musu rasuwa a aikin hajjin bana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta sanar da cewa, alhazan kasar su 49 aka tabbatar da rasuwarsu a aikin hajjin bana.

Bayanin ya ce tuni aka sanar da iyalan wadanda suka rasu, kuma bayan kamala aikin hajji za a gudanar da jazanarsu tare da sauran alhazan da suka rasu a lokacin aikin hajjin bana a kasar saudiyya.

Ahmad Ansari shi ne shugaban bangaren kiwon lafiya na hukumar alhazan kasar Masar, ya bayyana cewa, da dama daga cikin wadanda suka rasu sakamako ne na gajiya a lokacin jifar shaidan da kuma wasu amtsaloli na rashin lafiya.

Ya ce yanzu haka dai suna shirin dawo da sauran mahajjata da suka kamala aikin hajjin zuwa gida, kuma a bana babu wata matsala da aka fuskanta ta turmutsitsi wanda ya jawo mutuwar mutane a shekaru biyu da suka gabata.

3638286


captcha