IQNA

An Kama Abinci Da Aka Shirya Ba Bisa Kaida Domin Rabawa Ga Mahajjata

23:53 - August 30, 2017
Lambar Labari: 3481848
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a birnin Makka sun sanar da kame wani abinci har kwano dubu 5 da aka dafa kuma aka shirya ba bisa kaida ba da nufin sayar da shi ga alhazai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Makkah cewa, Khalid Sanadi magajin garin birnin makka yankin Umrah ya bayyana cewa, sun samu abincin wanda ya kai kwano dubu 5 wanda wasu masu wurin dafa abinci suka shirya ba tare da samun lasisin yin hakan ba.

Ya ci gaba da cewa jami’an tsaro sun kai sameme a wuraren bayan samun wani kwarmato kana bin da yake wakana a wurin, inda aka samu shiryeyyen abin da aka hada domin sayar da shi ga masu gudanar da aikin hajji.

Ya kara da cewa tun kafin wannan lokacin sun gargadi masu otel-otel kan sayen abinci daga wuraren dafa abinci da aka samar ba bisa kaida ba, domin hakan zai iya kawo matsala da kuma cutar da alhazai.

Yanzu gaka dai an kame mutaenen da suke da wannan wuri a cikin birnin makka, kuma za su gurfana a gaban kuliya domin fuskantar hukunci.

Alhazai da dama da suke zuwa gudanar da ayyukan hajji ko umara ba za su iya tantance wuraren cin abinci da suke ad lasisi da wadanda ba su da lasisi ba, wanda hakan kan baiwa masu gudanar da irin wannan sana’a sayar da abincins cikin sauki ga masu ziyara.

3636492

captcha