IQNA

An fara Gudanar Da Aikin Hajji A Yau

23:49 - August 30, 2017
Lambar Labari: 3481846
Bamgaren kasa da kasa, Alhazai da suak taru a Saudiyya domin sauke farali a bana, sun shiga aikin hajji gadan-gadan a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Maniyyatasama da miliyan biyu ne ake sa ran zasu bargarin Makkah zuwa Mina kafin su wuce zuwa Arfah, mafi muhimmanci ga aikin hajji, wanda shi ne haduwar mutane mafi girma a duniya.

Kafin hakan dai Saudiyya ta ce ta dauki kwararen matakai na tsaro inda aka tanadi dakaru sama da dubu dari domin tunkarar duk wata irin barazana dake iya tasowa.

Ko baya ga batun tsaro hukumomin lafiya na Saudiyya sun ce sun dau suk matakan da suka wajabadomin tunkarar barkewar cutuka ko annoba a lokacin wannan aikin hajjin.

A goda Alhamis ne ake hawan Arafa wanda shi ne kololuwar aikin hajjin.

A shekara dubu biyu da sha biyar data gabata alhazai kimanin dubu biyu ne sukayi shahada a yayin turmususun da aka samu a lokacin jifan shaidan.

Maniyatan Iran na daga cikin mahajatan na bana bayan sun kauracewa aikin hajji a bara saboda turmususun da aka samu.

3636322


captcha