IQNA

Baje Kolin Kur’ani Rubutun Hannu Na Morocco A Sharjah

23:45 - June 11, 2017
Lambar Labari: 3481600
Bangaren kasa da kasa, an bude wani baje koli na kwafin kur’anai da liffan addini rubutun hannu na kasar Morocco a birnin Sharjah na hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanmin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar sky news cewa, ma’aikatar kula da harkokin aladu a Sharjah da kuma ta kasar Morocco ne suke gudanar da wannan baje koli na hadin gwiwa.

Babbar manufar gudanar da wannan baje koli dai ita ce, nuna wasu daga cikin muhimman kayan tarihi na addinin muslunci, da suka hada da dadaddun kur’anai da aka rubuta da hannu gami da wasu littafan muslunci.

Kasar Morocco dai tana daga cikin kasashen musulmi da suke adana rubuce-rubuce daka yin a hannu da suka danganci addinin muslunci, inda a halin yanzutana da irin wadannan littfai masu kima masu tarin yawa.

Wannan baje koli dai yana gudana ne a babban dakin karatu na birnin Sharjah, inda ake samun masu zuwa birnin suna duba wannan baje koli mai kima.

3608459



Baje Kolin Kur’ani Rubutun Hannu Na Morocco A Sharjah

Baje Kolin Kur’ani Rubutun Hannu Na Morocco A Sharjah
captcha