IQNA

An Nuna Wasu Dadaddun Littafai A Hubbaren Imam Hussain (AS)

23:28 - March 06, 2017
Lambar Labari: 3481290
Bangaren kasa da kasa, an nuna wasu daddun littafai da kuma takardun gami da fatu da aka yi rubutu a kansu a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke Karbala a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Alfurat News ya habarta cewa, an fitar da wadannan kayan tarihi ne a karon farko, wadanda ba kasafai ake samunsu ba, domin kuwa daga ciki akwai wasu da ake danganta su da shi kansa Imam Hussain (AS).

Babbar manufar fitar da wadannan kayan tarihi dai ita ce kara gyara su da kuma kula da su domin ci gaba da adana su, ganin cewa wasu daga cikinsu sun fi shekaru dubu daya a wurin, wanda hakan yasa ala tilas a ci gaba da kula da su da kuma gyara su.

Wannan aiki yana da bukatar kwararru a kan harkar gyaran kayan tarhi, wanda hakan ne ya sanya wata tawaga ta musamman daga kasar Italiya a karkashin jagorancin Macor Dabila kwarre kan harkar adana kayan tarihi da kuma yin musu kwaskwarima.

Wannan tawaga ta duba wadannan kayayaykin da na’urori na zamani, domin sanin ta yadda za a fara gudanar da aikin gyara wadanda suka samu matsala daga cikinsu sadoda a jiya.

Manaf Al-tamimi shi ne babban daraktan bangaren kula da harkokin kayan tarihi na hubbaren Imam Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa wannan aiki yana bukatar kwararru, ganin cewa kayan suna da kima ta fuskoki daban-daban, ta fuskar tarihi da kuma wdanda ake danganta wadannan rubuce-rubuce zuwa gare su.

3581179

captcha