IQNA

An Fasa Nada Musulma A Matsayin Firayi Minista A Romania

21:47 - December 28, 2016
Lambar Labari: 3481078
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Romania Klaus Iohannis ya ki amincewa da sunan wata mata musulma wadda jam'iyyar masu ra'ayin sauyi na gurguzu na kasar ta gabatar masa a matsayin wadda suke so ya nada ta a matsayin firayi ministan kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Press TV cewa, rahotanni daga kasar Romaniyan sun bayyana cewar a jiya Talata ce shugaban kasar ya sanar da rashin amincewarsa da nadaSevil Shhaideh a matsayin firayi ministan kasar kamar yadda jam'iyyar PSD din ta ba da sunanta.

Shugaba Iohannis dai bai fadi dalilin kin amincewa da nadinta ba, to sai dai wasu wadanda suke adawa da nadin nata suna cewa ba ta da kwarewar rike wannan mukamin na firayi minista lamarin da wasu suke ganin ba haka ba ne.

Shugaban jam'iyyar PSD din Liviu Dragnea ya yi watsi da wannan mataki da shugaban ya dauka yana mai cewa akwai yiyuwa su dubi yiyuwar tsige shi daga shi daga karagar mulki.

Idan dai da shugaban ya amince da nada ta, to da za ta zama musulmi na farko da zai rike wannan mukami a kasar ta Romaniya.

3557255


captcha