IQNA - Qasem Moghadadi, makarancin kasar Iran, ya gabatar da karatun kur’ani a cikin ayarin Arba’in ta hanyar tattakin Arba’in da kuma jerin gwano da dama, ciki har da hubbaren Imam Husaini (AS).
IQNA - A jawabin da ya gabatar a wajen taron Gaza da aka yi a birnin Istanbul, babban jami'in kula da harkokin addini na kasar Turkiyya ya jaddada cewa, batun Kudus da Gaza bai shafi Falasdinawa kadai ba, lamari ne da ya shafi dukkanin musulmin duniya.
IQNA - Rukunin farko na alhazan Iran da suka gudanar da aikin Umrah bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2025 sun tashi daga tashar Salam na filin jirgin sama na Imam Khumaini zuwa Madina da safiyar yau Asabar.
IQNA - Da Hadisin Silsilar Zinare Imam Rida (AS) ya kafa hujja ga dukkan malaman bangarorin biyu dangane da wajibcin amincewa da Imamancin Ahlul Baiti (AS) da wajabcin yi musu da’a, da cewa tauhidi ba shi da ma’ana sai da wilayarsu.
IQNA - Ministocin gwamnatin Holland da dama daga jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin mazan jiya sun yi murabus a yammacin jiya Juma'a saboda rashin jituwa kan manufofin gwamnati kan Tel Aviv sakamakon yakin Gaza.
IQNA - Al'ummar birnin Landon na kasar Britaniya sun gudanar da gagarumin gangami domin yin Allah wadai da killace yankin Zirin Gaza da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi wanda ya haifar da yunwa a yankin Falasdinu.
IQNA - Annabcin manzon Alah Muhammad (SAW) ana daukarsa a matsayin canji mai inganci a tarihin dan Adam, domin ya dora wa mutum amana kuma shiriyar Ubangiji ta kare.
IQNA - Raja Umhadi ta ce: An tattauna batutuwan da suka shafi mata da matsayinsu a cikin iyali da zamantakewa ta bangarori daban-daban. Tunani da umarni na Musulunci wadanda suka bayyana a cikin al'ada da rayuwar Manzon Allah (SAW) suna nuni ne da irin rawar da mata suke takawa a Musulunci.
IQNA - Imam Hasan (AS) wanda ya kasance yana sane da abubuwan da suka faru, ya san cewa mabiyansa za su sha wahala matuka da irin barnar da Banu Umayya suka yi, don haka ya karbi zaman lafiya da farko domin amfanin Musulunci, na biyu kuma domin amfanar mabiyansa da masoyansa.
IQNA - Shugaban kungiyar ayyukan kur'ani mai tsarki na kwamitin kula da harkokin al'adu na Larabawa ya bayyana cewa: Bisa la'akari da tsawon kwanaki takwas na ayarin kur'ani mai tsarki a wannan shekara, an aiwatar da shirye-shiryen kur'ani fiye da dubu daya, wanda ya nuna karuwar kashi 5% a kididdigar.