Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, wannan faifan bidiyo ya fara ne daga aya ta 10 a cikin suratul Sajdah, kuma ya ci gaba har zuwa aya ta 14 na wannan sura, inda ake tafsirin ayoyin da harshen turanci.
A karshen kowane mataki na karatu, an yi taqaitaccen bayani kan muhimman batutuwa da ke tattare a cikin ayoyin da ake karantawa a qarqashin taken “Abin da muka koya daga wadannan ayoyin” kuma tsawon wannan shirin na mintuna 12 ne.