IQNA

Taimakawa mabukata agaji daga wani masallaci a Najeriya

14:21 - November 07, 2022
Lambar Labari: 3488138
Tehran (IQNA) Babban Masallacin Kwalejin Jihar Kaduna da ke Najeriya ya bayar da tallafin shinkafa da tsabar kudi Naira 577,000 ($1,333) ga mabukata.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Blue Print cewa, Aminu Yusuf Abdullahi limamin masallacin tsakiya kuma shugaban wannan kwalejin gwamnati, an bayar da wadannan tallafin ne ga mutane da suka hada da majiyyata, tsofaffi maza da mata, zawarawa, gajiyayyu da marasa galihu.

Ya kara da cewa ana bayar da wadannan tallafin ne ta hanyar gudunmawar da masu ibada ke karba tsakanin Sallar Magariba da Isha a duk ranar Juma’a da Asabar.

Ya ce: Wannan ita ce gudunmawar irin wannan ta biyar, kuma ya zuwa yanzu, sau uku ana bayar da gudummawar zakka ga mabukata.

Wannan wani shiri ne da Babban Masallacin Kwalejin Gwamnati na Jami’ar Gwamnati ke shiryawa ta kananan kwamitocinsa domin taimakawa mabukata da marasa galihu na al’umma.

Kaduna babban birnin jihar ne mai suna a arewacin Najeriya.

 

4097667

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kaduna najeriya taimaka mabukata agaji
captcha