IQNA

Makaranta Kur’ani Na Kungiyar Taha A Pretoria

23:45 - June 10, 2018
Lambar Labari: 3482744
Bangaren kasa da kasa, gungun makaranta kur’ani na Taha sun isa kasar Afirka ta kudu inda suka gudanar da karatu a Pretoria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar bunkasa al’adun musulunci cewa, karamin ofishin jakadancin Iran ne ya dauki nauyin gudanar da karatun.

Wannan gungun makaranta kur’ani na kungiyar Taha dukkaninsu dai ‘yan kasar Iran ne, wadanda suke karanta kur’ani da murya daya a lokaci guda.

Ana gayyatar s a kasashen duniya domin halartar taruka na addini, musamman a lokutan azumin watan Ramadan mai alfarma.

Sun gudanar da irin wannan karatu a wani masallaci a birnin Johannesburg na kasar ta Afirka ta kudu a daidai lokacin haihuwar Imam Hussain (AS).

Shugaban gungun dai shi ne Hussain Qurbani, wanda cibiyar yada ala’adun musulunci take hada gwiwa da shi domin gudanar da irin wadannan shirye-shirye na kur’ani.

3721667

 

 

 

 

captcha