IQNA

An Canja Wa Sheikh Zakzaky Wurin Da Ake Tsare Da Shi

22:14 - December 11, 2016
Lambar Labari: 3481025
Bangaren kasa da kasa, bayanai daga Najeriya sun jami’an tsaron kasar sun canja wa sheikh Ibrahim Zakzaky wurin da ake tsare da su zuwa wani wuri na daban da ba a sani ba.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin tashar Press TV cewa, jami’an tsaron Najeriya sun canja wa sheikh Ibrahim Zakzaky wurin da ake tsare da su zuwa wani wuri na daban da ba a sani ba a cikin birnin Abuja fadar mulkin kasar.

A farkon watan Disamn nan ne dai babbar kotun kolin kasa da ke Abuja ta bayar da umarnin da a saki sheikh Ibrahim Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

Bayan ‘yan kwanaki da yin haka sai gwamnatin jahar Kaduna ta fito ta bayyana harka Islamiyya a matsayin kungiyar yan tawaye.

Kafin wannan lokacin dai gwamnatin ta jahar Kaduna bayan fitar da sakamakon bincike da kwamitin da ta kafa kan rikicin Zaria ya yi, ta sanar da cewa ta haramta kungiyar baki daya.

Gwamnatin Kaduna ta dauki wannan mataki ne bayan da aka zargi sojoji da yin kisan gilla a kan mutane fiye da dari uku, tare da neman a hukunta su, duk kuwa da cewa har yanzu babu maganar binciko wadsanda suka aikata hakan daga gwamnatin kaduna ko ta tarayya.

Tun a ranar 14 ga watan Disamban shekara ta 2015 ne dai jami’an sojin Najeriya suka kame sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa, bayan kasha ‘ya’yansa uk da kuma daruruwan mabiyansa, inda a hukunce gwamnatin kaduna ta amince da kasha mutane kusan 350 a lokacin, yayin da adadin jerin sunayen mutanen da sojoji suka kasha a wurin da harka ta fitar yah aura mutane dubu daya.

A cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma jami’an ‘yan sanda sun kasha mutane kimanin 100 a lokacin da suke shirin yin tattakkin arbaeen daga kano zuwa zaria domin tunawa da ranar cika kwanaki arba’in na ashura, lamarin da jami’an tsaron suka kasha jama’a a kansa.

3552738


captcha