Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Ahlul
bait cewa, wasu daga cikin mambobin harkar muslunci a Najeriya sun gana
da wasu daga cikin yan majalisar dokokin najeriya, inda suka bukaci cewa
dole ne a kafa kwamiti wanda zai bi kadun abin da ya faru, kan kisan
yan shia da kuma kame sheikh Ibrahim zakzaky.
Bayanin ya ci gaba da
cewa tun bayan kai harin da sojojin Najeriya suka yi a kan mabiya
mazhabar shi'a tare da kashe adadi mai yawa na mabiya mazhabar shi'a
karkashin jagorancin malamin da kuma almajiransa.
A kwanakin baya ne
dakarun sojin Najeriya suka kai hari kan Husainiyyar Bakiyyatullah da ke
birnin zaria ta mabiya mazhabar shi'a, inda suka kasha wasu daga
cikinsu, kamar yadda kuma suka kai wani harin a gidan sheikh Zakzaky,
tare da kasha dukaknin mutanen da suka samu a gidansa tare da kame shi.
Har
yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta bayar da wani bayani takamamai kan
dalilin yin wanan kisa na daruruwan fararen hula da bas u dauke da
makamai ba, illa dai kawai suna bayar da hujjar cewa an tare hanyar
shugaban sojoji nea lokacin da yake wucewa.
3471677