IQNA

An Girmama Mata Mahardata Kur’ani Mai tsarki A kasar Turkiya Baki Dayansa

17:49 - July 21, 2012
Lambar Labari: 2373891
Bangaren kur’ani, an gudanar da wani zaman taro na girmama wasu daga cikin matan da suka hardace kur’ani mai tsrki a masallacin Malik Yalo da ke garin Yalo a cikin kasar Turkiya tare da halartar malaman addinin Musulunci da kuma wakilai na cibiyoyin addinin muslunci da suke garin kamar dai yadda rahoton ya bayyana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahabarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zaman taro na girmama wasu daga cikin matan da suka hardace kur’ani mai tsrki a masallacin Malik Yalo da ke garin Yalo a cikin kasar Turkiya tare da halartar malaman addinin Musulunci da kuma wakilai na cibiyoyin addinin muslunci da suke garin kamar dai yadda rahoton ya bayyana ga manema labarai.
Wasu masu bin diddigin lamurran da suke faruwa na siyasar kasashen larabawa sun imanin cewa, Muhammad Mursi yana da babban kalu bale a gabansa, kasantuwar cewa da dama daga cikin mutanen da suka jefa masa kuri'a suna da fatan ganin ya yanke alakar kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da taimaka ma al'ummar palastinu, sabanin gwamnatin Husni Mubarak da ta kasance babbar kawa ga Isra'ila, da ake hada baki da ita wajen cutar da al'ummar palastinawa.
Bugu da kari kan hakan, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
Yanzu dai za a iya cewa kasashen Amurka da sauran kawayenta larabawa musamman Saudiyya, suna baiwa Mursi rata ne domin su ga kamun luddayinsa, idan har zai iya tafiya da salon siyasa da zai kare manufofinsu, ko da kuwa bai kai kamar yadda babban aminsu Husni Mubarak ya kasance yanayi ba, to za su iya daga masa kafa, a matsayin rashin uwa a kan yi uwa daki.
1057411

captcha