Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar ta Al-Azhar Observatory da ke yaki da tsattsauran ra'ayin kin jinin musulunci a duniya musammana anahiyar turai, bayan harin da aka kai kan wata mata Musulma mai juna biyu a Italiya, ta yi gargadi kan karuwar wadannan hare-hare, saboda yaduwar kyamar musulunci daga bangaren masu tsattsauran ra'ayi.
A wannan harin, wani dan kasar Italiya mai shekaru 35 ya ci zarafin wata mata Musulma a lokacin da suka shiga jirgin kasa a gaban danta mai shekaru 11.
Mutumin dan kasar Italiya ya ci gaba da fadin kalaman wariya da cin zarafi a kan matar musulma.
Cibiyar sa ido ta Al-Azhar ta bayyana cewa: bisa ga abin da 'yan sandan Italiya suka sanar, an kama wannan mutumi kuma yanzu haka yana fuskantar tuhuma da laifin kai hari da gangan da kuma cutar da wannan mata dad anta karami.
Haka nan kuma cibiyar ta yi ishara da karuwar irin wadannan ayyuka da musulmi suke fuskanta a cikin kasashen turai daban-daban, wanda ta bayyana hakana amatsayin lamari mai matukar hadari, da ke bukatar hukumomin wadannan kasashe su mike haikan domin kare musulmi ‘yan tsiraru da suke rayuwa a wadanna kasashe.