IQNA

An fitar da tsari na digital mai yin jagora kan ayyukan Hajji a cikin harsuna 14

14:22 - July 02, 2022
Lambar Labari: 3487495
Tehran (IQNA) Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da tsari mai yin jagoranci na gani da sauti guda  13 na ayyukan Hajji daban-daban a cikin harsuna 14 don saukaka gudanar da wadannan ayyukan.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Siddati cewa, wannan ma’aikatar ta fitar da sanarwa a jiya, 1 ga watan Yuli, inda ta sanar da cewa: Wadannan shirye-shirye na gani da na sauti suna samar da dukkanin bayanan shari’a, kiwon lafiya, gudanarwa da kuma al’adu da suka shafi aikin Hajji cikin sauki da kuma hotuna masu motsi.

Haka nan kuma da zane-zane na Alhazai  ke bayyana yadda ake yin aikin, ta yadda  za a iya amfani da tsarin  cikin sauki.

Waɗannan jagororin sun haɗa da jagorar Ihrami, lafiya da tsafta, bayanai game da sassa daban-daban na Masallacin-ul-Nabi, jagoran hidima na Masjidul-Nabi, Ramyul  Jamrat, ranar Arafah, Muzdalifah, jagorar ibadar Mina, ranar Eid al-Adha, Makkah.

Haka nan kuma  wurare masu mahimmanci, abubuwan tarihi na Madinah da yawon buɗe ido, jagoran Umrah da kuma hanyar zuwa Masallacin Harami.

Alhazai na iya komawa shafin  yanar gizon ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya don amfani da wadannan tsari,  kuma yana yiwuwa a nuna wadannan tsare-tsare  akan dukkan tsarin wayar salula a kowane lokaci da wuri, a kyauta.

An samar da waɗannan tsare-tsare ne daidai da manufofin Saudiyya don sauƙaƙe hidima ga mahajjata da amsa tambayoyin alhazai game da ayyukan Hajji a cikin harsuna 14, Larabci, Ingilishi, Faransanci, Urdu, Bengali, Indonesian, Malaysian, Hausa,. Amharic, Farsi, Sipaniya,Turkanci,  Rashanci da Kuma Sinhalese.

4067905

 

 

 

captcha