IQNA

Musulmin Uganga ba su amince da sayar da naman alade a  kusa da makabrtarsu ba

14:15 - July 02, 2022
Lambar Labari: 3487494
Tehran (IQNA) Musulman Uganda sun yi Allah wadai da yadda ake sayar da naman alade a kusa da kaburburan Musulunci na wannan kasa tare da neman a dakatar da wannan mataki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, majalisar koli ta musulmin kasar Uganda (UMSC), ‘yan majalisar musulmin kasar da kuma shugabannin musulmin kasar sun yi tir da matakin da masu sayar da naman alade a kusa da makabartar musulmi suka yi a ranar Juma’a 10 ga watan Yuli.

'Yan majalisa da shugabannin musulmi sun ce masu sayar da naman alade ba sa damuwa su kawo kasuwancin su kusa da makabarta, ko da kuwa na musulmi ne.

Kakakin UMSC Ashraf Movala ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, wannan matakin na iya haifar da muzgunawa musulmi da rikici.

 فروش کباب خوک در مجاورت آرامگاه اسلامی اوگاندا

Ya ci gaba da cewa: Abin da suke yi yana da muni kuma yana iya haifar da rigingimun addini. Majalisar hadin gwiwar addinai ta kasar Uganda mai mabiya darikar addinai, ta gudanar da wani taro inda ta bayyana cewa ya kamata al'ummar Uganda su mutunta addinin juna. A wannan taron an kuma sanar da cewa, masu sayar da naman alade kusa da kaburburan Musulunci su daina wannan tada hankali.

Su ma 'yan majalisar musulmin kasar Uganda sun bayyana cewa wannan matakin cin fuska ne ga addinin muslunci kuma ya kamata a gaggauta dakatar da shi.

Wannan mummunan abu ne," in ji dan majalisar Swadi Keitanya. Kowa ya mutunta addinin juna.

Muhammad Kato, wakilin al'ummar yankin Mbirizi ya kuma ce: Ya kamata shugabannin kasar Uganda da shugabannin dukkanin addinai na kasar nan su koyar da mutane mutunta addinin juna tare da kaucewa gaba da juna.

Sheikh Sadat Bedulah, alkalin gundumar Bayukoh, ya kuma ce sayar da naman alade a inda musulmi suke tare da sauran al’umma, cin mutunci ne don haka ya bukaci hukumomi da su amince da dokar sayar da naman alade a wuraren taruwar jama’a.

 

https://iqna.ir/fa/news/4067939

 

captcha