IQNA

Kakakin Nujba: Juyin Musulunci A Iran Ya Dakushe Kumajin ‘Yan Mulkin Mallaka A Duniya

21:57 - February 08, 2022
Lambar Labari: 3486927
Tehran (IQNA) kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Nujba a Iraki ya bayyana juyin juya halin musulunci a Iran a matsayin babban abin da ya dakushen kumajin ‘yan mulkin mallaka masu girman kai.

A lokacin da yake gabatar da jawabi kai tsaye ta hanyar yanar gizo a taron kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran, kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Nujba a Iraki Nasr Shummari ya bayyana juyin juya halin musulunci a Iran a matsayin babban abin da ya dakushen kumajin ‘yan mulkin mallaka masu girman kai na duniya.

Ya ci gaba da cewa, kafin samun nasarar juyin jya halin musulunci a Iran, manyan kasashe masu girman kai suna cin karensu babu babbaka, domin kuwa wata kasa da ta isa ta ce musu uffan, kuma abin da suka ga dama shin ne ake yi a dunya.

To amma bayan samun wanann juyi, lamurra da dama sun juya a duniya, ta fuskar siyasa da kuma hatta batutuwa na tsaro a mataki na kasa da kasa, domin kuwa a lokacin ne irin wadannan kasashe musamman Amurka, suka fahimci cewa ba kullum ne suke iya yin nasara wajen kare gwamnatocin kama karya ba.

Wannan babban abin da yasa tun daga lokacin Amurka da wasu daga cikin kasashen turai suka dauki karan tsana suka dora ma Iran, alhali kafin wannan lokacin babu wata kasa a yankin gabas ta tsakiya da Amurka ke dasawa da ita kamar Iran, in banda Isra’ila, ko Saudiyya a lokacin sai ta yi kamun kafa da Iran kafin ta samu wani abin daga Amurka ko yahudawa.

Kawar da tsarin kama karya na sarautar Shah da Amurka da Isra’ila suke marawa baya, ya canja yanayin gabas ta tsakiya baki daya, kuma hakan ya karfafa gwiwar Falastinawa ‘yan gwagwarmaya wajen mikewa domin kwatar hakkokinsu da aka raba su da su bisa zalunci.

Babban abin da ya kara karfafa gwiwar Falastinawa shi ne, yadda juyin musulunci ya kasance yana dauke da akidar ‘yantar da Falastinu daga mamayar yahudawa, da kuma kubutar da masallacin Quds maialfarma daga hannun yahudawa.

Baya ga haka kuma wannan juyin ne ya kawo cikas kuma ya zama babban karfen kafa da hana Amurka da Isra’ila cimma manufofinsu a kasashen musulmi musamman a  yankin gabas ta tsakiya, domin idan a lokacin baya babu wata kasar da za ta iya taka musu burki, to yanzu akwai, ita ce bayan juyi.

4034578

 

 

 

captcha