IQNA

An Kammala Aikin Gyaran Wani Tsohon Kur'ani Da Aka Rubuta Shekaru Fiye Da Dubu Da Suka Gaba

23:53 - June 20, 2021
Lambar Labari: 3486031
Tehran (IQNA) an kammala gudanar da aikin gyaran wani tsohon kwafin kur'ani mai tsarki a kasar Uzbakestan.

Kamfanin dillancin labaran Azar Taj ya bayar da rahoton cewa, an kammala aikin gyaran wani tsohon kwafin kur'ani mai tsarki a kasar Uzbakestan wanda tarihin rubutunsa ke komawa zuwa ga fiye da shekaru dubu daya da dari biyu da suka gabata.

Masana kan gyaran tsoffin kwafin takardu an tarihi ne suka gudanar da aikin wanda aka gudanar a mataki uku, daga cikinsu har da wasu fitattun masana a wanann fage daga dakin ajiyar kayan tarihi na Louvre na kasar Faransa da aka gayyata domin gudanar da wannan aiki.

An kammala aikin amataki na farkia  cikin watan Nuwamban 2019, sai kuma mataki na biyu a cikin watan Fabrairun 2020, mataki na karshe kuma a cikin watan Mayun da ya gabata.

ترمیم یکی از قدیمی‌ترین نسخه‌های قرآن در ازبکستان

 

3978512

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tsohon
captcha