Jaridar Quds Al-rabi ta bayar da rahoton cewa, dubban mutanen kasar Morocco ne suka shiga cikin wani kamfe na neman a kori shugaban ofishin wakilci na Isra'ila da ke kasar ta Morocco.
Rahoton cewa, wasu masu fafutuka ne suka kaddamar da kamfe din a shafukan sada zumunta na yanar gizo, wanda kuma ya samu karbuwa matuka atsakanin mutanen kasar.
Wannan kamfe dai an kaddamar ad shi ne bayan yakin da Isra'ila ta kaddamara kan al'ummar Gaza a cikin 'yan makonnin da suka gabata.
Morocco dai tana daga cikin kasashen larabawa da suka kulla alaka da Isra'ila, biyo bayan matsin lambar da gwamnatin Ammurka ta yi a kansu.