IQNA

Littafin (In My Mosque) Na Daga Cikin Littafan Da Aka Fi Yin Cinikinsu Ta Hanyar Yanar Gizo

17:52 - February 20, 2021
Lambar Labari: 3485672
Tehran (IQNA) littafin In My Mosque yana daga cikin littafan da aka fi yin cinikinsu ta hanyar cinikayya a yanar gizo a shagon Amazon.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, tun bayan harin ta’addancin da aka kai a kan masallaci a kasar New Zealand tare da kashe musulmi a cikin shekara ta 2019, Mvnvar Avlgvn Yuksel musulmi dan kasar Turkiya da ya hijira zuwa kasar Amurka ya rubuta wannan littafi, domin amfanin kananan yara.

A cikin littafin nasa dai ya yi kokarin bayyana abubuwa masu daukar hankali matuka dangane da addinin muslunci, da kuma yadda wasu da dama ba su fahimci kyakkyawar koyarwa irin ta addinin muslunci, wanda hakan ne yasa suke kin wannan addini da yake koyar da zaman lafiya da tausayawa, da jin kai ga dan adam.

Haka nan kuma a wasu bangarori na littafin ya fito da matsayin addinin muslunci kan abubuwa da dama da suka shafi rayuwa ta zamantakewar al’umma, wanda yake nuni da cewa shi musulunci ne yake tafiya tare da kowa da kuma kyautata wa kowa hatta wadanda ba musulmi ba, domin shi addini ne na ‘yan adamtaka.

Baya haka kuma ya bayyana irin abubuwan da ake yi a cikin masallatai na musulmi da cewa abubuwa na ibada da suke da alaka da karfafa ruhin dan adam, da samun natsuwa, da kuma daukar darussa na kyawawan halaye wadanda su ne kowace al’umma take bukata domin kyautata zamantakewarta.

Wadannan muhimman bubuwa da littafin ya kunsa, ya sanya hatta wadanda ba musulmi ba suna nemansa domin karanta shi da kuma karuwa da abubuwan da ke cikinsa.

3955043

 

captcha