IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah:

Akwai Bukatar Daukar Matakai Na Karfafa Tattalin Arziki Maimakon Dogaro Da Yammaci

23:41 - July 08, 2020
Lambar Labari: 3484966
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa komawa zuwa ga gabashi baya nufin yanke alaka da yammaci, amma yana da kyau a karfafa dogaro da kai.

Babban sakataren kungiyar Hizbulah ta kasar Lebanon sayyeed Hassan Nasarallah, ya bukaci mutanen kasar su koma gona da kuma gina masana’antu don fuskantar barzanar da kasar ta fada ciki na rugurgujewar tattalin arziki.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto Sayyeed Nasarallah yana fadar haka a jawabinda da ya gabatar kai tsaye ta gidadajen talabijin da kafafen sadarwa a dama a jiya Talata.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa “daga yau zamu dauki ranar 7 ga watan ga yulin shekara ta 2020 a matsayin ranar da muka kaddamar da “Jihadin Noma da Kafa masana’antu a kasar Lebanon”.

Malamin ya kara da cewa, kamar yadda muka sami nasarori a jihadin da muka kutsa a shekarun da suka gabata, wadanda suka hada da jihadi da HKI, Jihadi da ‘yan ta’adda masu kafirta mutane a kasar Lebanon da kuma Siriya, to da yardar All.. a cikin wannan jihadi na Noma da kafa masana’antu ma zamu sami nasara.

Sayyeed nasarallah ya ce, tare da wannan shirin ko kuma jihadin, ba zamu mutu saboda ‘yunwa ba, kuma zamu rayu a matsayin ‘yentattun mutane. A cikin yan makonnin da suka gabata ne gwamnatin kasar Amurka ta dorawa kasar Siriya takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar, wadanda suka shafi a kasar ta Lebanon, a dai-dai lokacin da darajar kudaden kasar suka fadi warwas.

 

 

3909304

 

 

 

captcha