IQNA

‘Yan Ta’addan Daesh Ne Ke Da Alhakin Kisan Hisham

23:48 - July 07, 2020
Lambar Labari: 3484963
Tehran (IQNA) Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kisan fitaccen masanin harkokin tsaro a kasar Iraki Hisham Alhashimi a daren jiya.

Kamfanin dillancin labaran Bagdad News ya bayar da rahoton cewa, a cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta fitar, ta tabbatar da kisan Hisham Alhashimi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren jiya ne wasu mutane da ba a san ko suwane da suka rufe fusakunsu, suka bude wa Hisham wutar bindiga alokacin da yake dawowa gidansa kafin ya fita daga cikin motarsa, ya kuma rasa ransa jim kadan bayan isa da shi zuwa asibiti a cikin birnin Bagadaza.

Hisham dan shekaru arbain da bakawai da haihuwa, kwararre ne kan harkokin tsaro da kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda, kamar yadda kuma ya yi bincike mai zurfi kan lamurra na tsaro, inda ya rubuta littafai a wannan fage.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta fitar da sanarwa a yau cewa, ita ce ke da alhakin yi wa Hisham Alhashimi kisan gilla a daren jiya.

 

3909079

 

 

 

 

captcha