Rahotanni daga Najeriya sun sun ce a cikin wata sanawa da bangaren kula da harkokin jigilar alhazai a Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa kamfanonin da suke jigilar alhazai a kasar za su tafka asara a bana wadda za ta kai ta kimanin dalar Amurka miliyan 400, sakamakon rashin halartar alhazai daga Najeriya a wannan shekara.
Bayanin ya ce an karbi kudade daga maniyyata da dama da suke nufin gdanar da aikin hajjin bana, wanda kuma abin da ya biyo baya ya sanya dole a mayar musu da kudadensu.
Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa wasu kamfanonin sun yi amfani da kudaden wajen shirye-shiryensu kamar yadda suka saba yi a kowace shekara, wanda hakn ke nufin sun yi asara.