IQNA

Zarif: Matsayar Kasashen Turai A Hukumar IAEA Za Ta Kawo Cikas Ga Yarjejeniyar Nukiliya

23:43 - July 04, 2020
Lambar Labari: 3484951
Tehran (IQNA)Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, matsayar da manyan kasashen turai uku suka dauka a kan Iran a zaman alkalan hukumar IAEA, zai iya kawo babban cikas ga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musawi ya sanar da cewa, a jiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif, ya aike da wani sako zuwa ga babban jami’i mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Joseo Borrell.

A cikin sakon nasa, Zarif ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen Jamus, Burtaniya da kuma Faransa suka dauki wani mataki a hukumar IAEA, wanda a cewarsa hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar da suka cimmawa tare da Iran.

Haka nan Zarif ya kara da cewa, daukar irin wannan mataki na siyasa wanda bai da alaka da kwarewa, ba zai amfanar da kowane bangare daga cikin bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar ba.

Kasashen turan uku, wato Jamus, Burtaniya da kuma Faransa, sun gabatar da wani daftarin kudiri da ke sukar Iran a zaman kwamitin alkalan hukumar makamashin nukiliya ta duniya, da nufin yin amfani da hakan wajen amincewa da bukatar da Amurka ta gabatar, ta neman a sabunta takunkumin hana saye da kuma sayar wa Iran da makamai a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.

Sai dai kasashen Rasha da China sun yi watsi da bayanin kasashen turan a hukumar IAEA, kamar yadda kuma suka yi watsi da daftarin kudirin Amurka a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan batun na Iran.

ha.abna24.com

captcha