IQNA

Kawancen Kungiyoyi Da Cibiyoyi Domin Yaki Da Kyamar Musulmi A Canada

15:44 - November 17, 2019
Lambar Labari: 3484249
An kafa wani kawance na kungiyoyi 30 domin yaki da nuna kyama ga musulmi a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalato daga shafin muslim link cewa, a birnin Otawa na kasar Canada kafa wani kawance na kungiyoyi 30 domin yaki da nuna kyama ga musulmi a kasar.

Jimm Watson shi ne magajin garin birnin Otawa wanda ya halarci zaman taron ya bayyana cewa, yana burin ganin an samu wani shiri makamancin hakan, domin ganin an kawo karshen nuna kyama ga musulmi da cin zarafin mata da kabilanci da abubuwa da suka kama da haka.

Amira Alghawabi daya ce daga cikin musulmi mata masu fafutuka a kasar ta Canada da suke gwagwarmaya domin kae hakkokin musulmi, ta bayyana cewa daukar wannan mataki zai taimaka matuka wajen shawo kan wannan matsala da musulmi suke fuskanta.

Bisa ga sanarwar jami’an ‘yansandan birnin, nuna kyama ga musulmi ya karu da kashi 67% daga shekara ta 2017 ya zuwa shekarar da muke ciki.

3857455

 

captcha