IQNA

Zaman Taron Malaman Gwagwarmaya

15:40 - November 17, 2019
Lambar Labari: 3484248
Bangaren kasa da kasa, a gefen taron makon hadin kan musulmi a gudanar da taron malaman gwagwarmaya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a jiya Asabar a gefen taron makon hadin kan musulmi a gudanar da taron malaman gwagwarmaya inda Ayatollah Araki shugaban cibiyar kusanto daga mazhabaobin muslunci ya gabatar da jawabi.

A cikin jawabin nasa ya karfafa wajabcin ci gaba da sauke nayin da ya rataya a kan malaman addinin muslunci, wajen ganin an kusato da fahimta tsakanin al’ummar musulmi da dukkanin bangarorinta.

Ya ce dunkulewar al’ummar musulmi wuri guda shi ne daukakarta, yayin da rarrabuwa da sabani da sukar juna saboda sabanin fahimta kan wasu na gefe, ba shi ne hakikanin abin da ya hada su ba, musulunci shi ne ya hada musumi ba mazhaba ko kungiyanci ko bangaranci ba, domin kuwa ko wane musulmi yana mazhabarsa yana kungiyarsa yana da irin tasa fahimtar.

Shi ma a nasa bangare ayatollah Taskhiri ya fadi a wurin taron cewa, babban abin da ke gaban al’ummar musulmia  halin yanzu si ne hadin kai, matuka suna son zama al’umma guda wadda manzon Allah zai yi alfahari da ita.

Kamar yadda kuma ya ja hankulan malamia da su guji tunzura magoya bayansu wajen yada kiyayya a tsakanin musulmi a junasu, domin kuwa musulmi ba makiyin musulmi ba ne, ko da kuwa sun samu sabain fahimta kan wata mas’ala ta addini.

3857556

 

captcha