IQNA

Masani Daga Mauritania: Dole Ne A Yi Koyi Da Ma’aiki Matukar Ana Binsa

12:13 - November 16, 2019
Lambar Labari: 3484247
Wani masani daga kasar Mauritania a zantawa da IQNA ya bayyana cewa, dole ne a yi koyi da ma’aiki matukar ana biyayya gare shi.

Sidi Muhammad Ja’afar wani masani daga kasar Mauritania a zantawa da IQNA a taron mkon hadin kai na 33 a Tehran, ya bayyana cewa dole ne a yi koyi da ma’aiki matukar ana biyayya gare shi a cikin dukkanin marinas.

Ya ce babbar matsalar musulmi a halin yanzu ita e koyi da ma’aiki ko ikirarin bin hakikanin sunnarsa ya zama magana da fatar baki, ta yadda a aikace muuslmi sukan bi son ransu da sunan adini.

Haka nan kuma ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin musulmi na duniya da ska seda cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Muhammad kuma manzonsa ne, wanda wannan ya kudirce wannan shi ne musumi.

Dangane da bambance bancen fahimta tsakanin musulmi kuwa ya bayyana cewa, babu yadda za  yi fahimtar dukkanin al’umma ta zo daya, domin kuwa ko lokacin manzo ana sabanin fahimta tsakanin musulmi, amma kasantuwarsa a raye shi ne ke waware komai.

Daga karshe ya jaddada wajabcin samun hadin kai tsakanin al’ummar musulmi, tare da ajiye banbancin fahimta a gefe domin ba shi ne addini ba, musulunci shi ne addini ba mazhaba ko mahanga ba ko ra’ayi ba.

 

3857276

 

captcha