IQNA

Rauhani: Ci Gaban Kasa Yana Tattare Da ci Gaban Iliminta

23:53 - November 11, 2019
Lambar Labari: 3484241
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa bunkasa ilmin kimiyya da fasaha a kasar ne mabudin ci gaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto shugaban yana fadar haka a birnin Yazd inda yake ziyarar aiki a jiya Lahadi, har’ila yau bayan taron majalisar shawara da birnin yazd.

Dr Rouhuni ya kara da cewa dangantaka tsakanin kungiyar kasashen Eurasia zai taimakawa kasar wajen bunkasa hanyoyin kasuwanci da kasashen duniya.

Shugaban ya bayyana shekaru 2 da suka gaba ne a kasar, a matsayin lokaci mafi tsanani ga mutanen kasar a tarihin juyin juya halin musulunci. Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa tana iyakar kokarinta don ganin kasar ta fita daga mummunan halin da take ciki, amma ba zata taba amincewa da daukar kaskanci ba.

Kaar Iran dai ta ce ba za ta sake shiga wata tattaunawa da Amurka ko wata kasa kan shirinta na makamai masu linzami.

 

3856416

 

 

 

 

 

captcha