Kamfanin dillancin labaran iqna, mahardata kur’ani daga cikin muuslmin kasar Birtaniya sun siga gasar share fage ta gasa mai zuwa.
A ranakun 14 da 15 ne dai za a kai ga mataki na karshe na wannan gasar kur’ani mai tsarki ta share fage a kasar ta Birtniya.
Bnagarorin da za a gudanar da gasar a cikinsu sun hada da bangare na juzui 5 da kuma juzui 15 da kuma juzui 30.
Wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin za su samu kyautuka da za su hada har da kudade.
Baya ga haka kuma daga cikinsu ne za a zabi wadanda za su wakilci kasar a gasar kr’ani ta kasa da kasa da ake sa ran gudanarwa a kasar ta Birtaniya.
Haka nan kuma baya ga kyautar kudade za a basu tikitin tafiya Haji da Umra kyauta domin sauke farali.