IQNA

Gwamnatin Sudan Na Shirin Mika Albashir Ga Kotun Duniya

21:50 - November 04, 2019
Lambar Labari: 3484222
Gwamnatin Sudan ta ce za ta mika tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya ruwaito cewa a wannan Litinin ce gwamnatin rikon kwaryar kasar Sudan ta sanar da cewa dukkanin manbobin gwamnati ciki har da Ibrahim Al-shekh shugaban jam'iyar Congres sun amince da bukatar kotun hukunta manyan-manyan laifuka ta Duniya na mika tsohon shugaban kasar Omar Al-bashir bayan kamala shari'ar da yake fuskanta a kasar.

Yayin da yake gabatar da taron manema labarai a wannan Litinin Ibrahim Al-Shekh ya ce tabbas za a mika Al-Bashir ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, sai bayan kamala shari'ar da yake fuskanta a babbar kotun birnin Khartum.

A halin da ake ciki dai tsohon shugaban kasar ta Sudan Omar Al-bashir na fuskantar tuhumar da zargin barnata dukiyar kasa da kuma wuce gona da iri wajen amfani da karfi a yayin da yake shugabancin kasar.

Bayan an yi masa juyin mulki, shugaba Al-bashir ya bukaci jagororin kasar da kada su mika shi ga kotun ICC.

Kotun ICC ta bayar da sammacin kame tsohon shugaban kasar ta Sudan ne bayan ta zarge shi da aikata laifukan yaki a yankin Darfur.

 

3854526

 

 

 

captcha