IQNA

Magoya Bayan Harkar Musulunci A Najeriya Sun Yi Tattakin Arbaeen

23:54 - October 19, 2019
Lambar Labari: 3484170
Magoya bayan harkar muslunci a Najeriya sun yi tattakin arbaeen a birnin Abuja fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya magoya bayan harkar muslunci a Najeriya sun yi tattakin arbaeen a birnin Abuja fadar mulkin kasar inda jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su.

Bayanin ya ce masu jerin gwanon sun daga tutoci masu dauke da rubuce-rubuce na addini kamar Kalmar shahada da kuma sunayen ahlul bait musaman Imam Hussain.

Jami’an tsaron dai sun yi amfani da karfi wajen tawatsa jerin gwanon, wanda suka bayyana da cewa ba ya bisa ka’ida.

Tun kafin wannan lokacin dai babban sufeton ‘yan sanda na kasar ya bayyana cewa ba su hana ‘yan shi’a gudanar da taruka ba, amma ban da harkar musulunci da ya ce an haramta a kasar.

Magoya bayan harkar musulunci dai sun dage a kan cewa sai sun yi jerin gwano a ranar arbaeen, saboda ‘yancin da kowa yake da shi a kasar na yin addini daidai fahimtarsa.

 

3850814

 

 

 

captcha