IQNA

Kalubalantar Dokar Nuna Kyama Ga Musulmi A Cuebec Canada

23:48 - July 12, 2019
Lambar Labari: 3483831
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kungiyoyin musulmi da masu kare hakkokin addinai sun shigar da kara kan nuna kyama gga addinin muslunci a Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu daga cikin kungiyoyin musulmi da masu kare hakkokin addinai sun shigar da kara kan nuna kyama gga addinin muslunci a jihar Cuebec da ke kasar Canada  a jiya.

Sun matakin ne bayan bayan kafa dokar da gwamnatin Jihar ta Cuebec ta yi ne, kan cewa dole ne malaman makarantu su cire duk wata sutura da addini a lokacin da suke cikin aiki.

Daga cikin ‘yan jarida wani ya tambayi gwamnan jihar kan wanann doka a kan ko za ta iya hawa kan kowa, y ace dole duk wata malama mace ta daina saka tufafi na addininta a lokacin karantarwa.

Wannan mataki dai yana shan suka daga kungiyoyin kare hakkokin mabiya addinai a kasar ta Canada, da kuma kungiyoyin kare hakkokin bil adama da dama a cikin kasashen duniya baki daya.

Dokar dai za ta fi shafar mata musulmi ne wadanda suke saka lullubi a kansu, inda hakan yake a matsayin wani sabon mataki na takura rayuwarsu a kasar ta Canada.

 

 

3825943

 

 

 

captcha