IQNA

Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Kasar Tanzania

23:31 - May 22, 2018
Lambar Labari: 3482683
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki da aka saba gudanarwa a kasar Tanzania a kowace shekara

.Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Afrika News ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Tanzania da ae gudanarwa a kowane watan Ramadan mai alfarma.

Gasar dai ana gudana da ita ne  a dukkanin bangarori na kira’a da kuma harda da kuma tajwidi gami da sauran bangarori da suka hada da tafsiri da sauransu.

Kasashe 20 ne dai suke halartar wannan gasa, mafi yawansu daga gabashin nahiyar Afirka sai kuma wasu daga tsakiyar Afrika.

3716622

 

 

captcha