IQNA

Kalubalantar Siyasar Kiyayya Da Palastinawa A Facebook

22:25 - February 22, 2018
Lambar Labari: 3482418
Bangaren kasa da kasa, masana harkokin yanar gizo daga cikin Palastinawa sun fara kalubalantar siyasar kin Palastinawa da kamfanin facebook ke nunawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Quds Arabi cewa, sakamakon irin matakan da kamfanin facebook ke dauka na nuna adawa da Palstinawa, ta hanyar takura ma shafukan da ke nuna goyon baya ga palastinu, Palastinawa masana sun fara daukar matakan kalubalantar wannan matsayi.

Daga cikin irin matakan da masana suke shirin dauka kuwa, har bullo da sabon kamfe da ke bayyana facebook a matsayin kamfani mai kiyayya da Palastinawa, domin kare siyasar zalunci ta yahudawa.

Haka nan kuma kamfe din zai dauki salo daban-daban, da hakan ya hada da yada Kalmar (#FBfightsPalestine) a shafukan facebook da na yanar gizo, haka nan kuma za su dauki matakai na shari’a domin fuskantar lamarin.

3693724

 

 

 

 

captcha