IQNA

Rawar da Kafofin Yada Labarai Za Su Taka Wajen Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi

23:51 - February 20, 2018
Lambar Labari: 3482414
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro a yau mai taken rawar da kafofin yada labarai za su iya takawa wajen yaki da tsatsauran ra’ayi a Nijar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na akhbar yaum cewa, an fara gudanar da wani zaman taro a yau mai taken rawar da kafofin yada labarai za su iya takawa wajen yaki da tsatsauran ra’ayin a birnin Yamai fadar mulkin kasar Nijar a yau Talata.

Wannan taro dai ya kebanci ‘yan jarida ne da masana kan harkokin yada labarai daga kasashen Afirka daban-daban, da suka hada da Aljeriya, Burkina Faso, Chadi, Najeriya, Nijar, Mali, Senegal Mauritania da Libya.

Mahalarta taron dai suna yin dubi ne kan irin rawar da ya kamata kafofin yada labarai su taka domin wayar da kan jama’a musamman ma matasa da ake yaudararsu da sunan addini suna shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci, suna kasha jama’a da sunan jihadi.

3693336

 

 

captcha