IQNA

Kasashe 70 Ne Za Su Halarci Gasar Kur’ani A Kasar Masar

23:55 - February 16, 2018
Lambar Labari: 3482402
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa kasashe 70 ne za su halarci gasar kur’ani ta kasa da kasa a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai vetogate.com ya bayar da rahoton cewa, Ashraf Fahmi daya daga cikin manyan daraktocin ma’aikatarkula da harkokin addni a Masar ya sheda cewa, kasashe 70 ne za su halarci gasar kur’ani ta duniya karo na ashirin da biyar da za a gudanar a kasar.

Ya ce ya zwa alkalai 10 aka tababtar da cewa za su yi alkalanci a gasar, dukkaninsu daga kasashen labawa.

Gasar dai za ta samu halartar wakilai daga kasashen larabawa da na musulmi da kuma kasashen Asia da na turai.

A ranar 24 ga watan Maris 2018  ne za a fara gudanar da gasar ta Masar, wadda za ta dauki tsawon kwanaki shida ana gudanar da ita.

3692000

 

 

 

 

 

captcha