IQNA

Shugaba Rauhani A Lokacin Sallar Juma'a A Haidar Abad:

Hadin Kan Al’ummar Musulmi Shi Kadai Mafita Ga Matsalolinsu

23:49 - February 16, 2018
Lambar Labari: 3482400
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar India ya bukaci musulmai a ko ina suke a duniya su hada kai don fuskantar makiyansu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaba Ruhani yana fadar haka a yau Jumma'a bayan sallar Jumma'a a birnin Haidar-abad na kasar ta India.

Kafin haka dai shugaban ya gana da Malaman addinin musulunci a birnin,  ya kuma ziyarci wuraren tarihi da kuma manya manyan jami'an gwamnati na yankin.

Dr Ruhani ya yi kira ga musulman kasar India su nun goyon bayansu ga mutanen kasar Palasdinu, ya kuma kara jaddada cewa matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na amincewa da birnin Qudus a matsayin cibiyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba abin amincewa bane ga musulmi.

Ana saran nan gaba a yau din shugaba Ruhani zai gana da Priministan kasar ta India Modi, da ministan harkokin wajen kasar da kuma manya manyan jami'an gwamnati da kuma yan kasuwa a birnin New Delhi.

Kasashen India da Iran dai suna da kyakyawar alaka ta kasuwanci da sauran bangarori na bunkasa tattalin arzikinsu, inda kasar ta India take a matsayin daya daga cikin muhimman kasashe da suke sayen danyen man fetur daga Iran.

Shugaba Rauhani dai zai ci gaba da gudanar da ziyarar tasa ne har tsawon kwanaki uku a kasa India, tare da ganawa da jami’an gwamnati da kuma masana gami da malamai na sunna da shi’a da suke a kasar, domin kara tabbatar da hadin a tsakanin al’ummar musulmi.

3692066

 

 

captcha